Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Al'teen: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 95 a Mushafi, ayoyi 8, tana farawa a shafi na 597.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'sharhSura Al'alaq ›

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.[1]

[1] Ibn Abbas ya ce: 'Attinu shi ne masallacin Nuhu a kan Judiyyi, Azzaitun Masallacin Baitil Muƙaddas.'.

2. Da Dũr Sĩnĩna.[1]

[1] Dutsen da Allah Ya yi magana da Musa a kansa. Ma'anarsa dutse mai albarka sabõda itacen da ke kansa.

3. Da wannan gari[1] amintacce.

[1] Gari amintacce shi ne Makkah.

4. Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.

5. Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni

6. Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.

7. To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?

8. Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?[1]

[1] Ana son wanda ya karanta sũrar har ƙarshe ya ce بلى ,wato na'am, Allah Ya fi kowa kyãwon hukunci.

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'sharhSura Al'alaq ›