Sura ta 111 a Mushafi, ayoyi 5, tana farawa a shafi na 603.
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1. Hannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka.
2. Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra.
3. Zã ya shiga wuta mai hũruwa.
4. Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta).[1]
[1] Anã fassara shi da mai tsegumi, wãtau annamĩmanci; da Lãrabci anã ce wã mai annamĩmanci "mai ɗaukar itacen wuta.".
5. A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma).
Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)
Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.