Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Al'takathur: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 102 a Mushafi, ayoyi 8, tana farawa a shafi na 600.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'qari'ahSura Al'asr ›

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (daga ibada mai amfaninku).

2. Har kuka ziyarci kaburbura.

3. A'aha! (Nan gaba) zã ku sani.

4. Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.

5. Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.

6. Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.

7. Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.

8. Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'qari'ahSura Al'asr ›