Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Al'asr: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 103 a Mushafi, ayoyi 3, tana farawa a shafi na 601.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'takathurSura Al'humazah ›

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. Ina rantsuwa da zãmani.[1]

[1] Wasu suna fassarawa da lokacin sallar La'asar da kuma marece. A kõwane dai, an bai wa lokaci muhimmanci, zãmani yana yanke wanda bai yanke shi ba. ba ya halatta ga mutum wata mudda ta zãmani ta wuce shi bai san amfãnin da ya sãma wa kansa a cikinta ba, kuma kõme ya sãmu idan ba addini ba ne, to, hasãrace.

2. Lalle ne mutum yana a cikin hasara.

3. Fãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri (su kam, basu cikin hasara).

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'takathurSura Al'humazah ›