Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Al'dhuha: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 93 a Mushafi, ayoyi 11, tana farawa a shafi na 596.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'lailSura Al'sharh ›

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. Inã rantsuwa da hantsi.

2. Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).

3. Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.

4. Kuma lalle ta ƙarshe[1] ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.

[1] Ta ƙarshe, wãto, Lãhira; kuma ta farko, wato, dũniya.

5. Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.

6. Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?

7. Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?

8. Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?

9. Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.

10. Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.

11. Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'lailSura Al'sharh ›