Sura ta 105 a Mushafi, ayoyi 5, tana farawa a shafi na 601.
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1. Ashe, ba ka ga yadda Ubangijin ka Ya aikata ga mutanen giwa[1] ba?
[1] An yi Yãƙin Gĩwa shekarar haihuwar Annabi tsakãnin halaka su da haihuwarsa kwãna hamsin. Bayan shekara arba'in Annabi ya fara karantar da mutane. Ya karantar da su cikin shekara ashirin da uku, sa'an nan ya ƙaura. Bayansa da shekara hamsin waanda suka bi shi suka cinye duniya. Wannan yana nuna cewa mutane ba su samun daraja sai da riƙon addini da ilimi.
2. Ashe, bai sanya kaidin su a cikin ɓata ba?
3. Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.
4. Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
5. Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?
Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)
Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.