Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Al'adiyat: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 100 a Mushafi, ayoyi 11, tana farawa a shafi na 599.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'zalzalaSura Al'qari'ah ›

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.

2. Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.

3. Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.

4. Sai su motsar da ƙũra game da shi.

5. Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.

6. Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

7. Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka.

8. Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.

9. Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.

10. Aka bayyana abin da ke cikin zukata.

11. Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'zalzalaSura Al'qari'ah ›