Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Al'nas: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 114 a Mushafi, ayoyi 6, tana farawa a shafi na 604.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'falaq

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. "Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."

2. "Mamallakin mutane."

3. "Abin bautãwar mutãne."

4. "Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa."[1]

[1] Shaiɗan yakan ɓõye idan ya ji an ambaci sunan Allah, dõmin haka aka yi masa suna mai ɓõyewa, wãto bã ya zuwa wurin da ake karatu da wa'azi, kamar yadda bã ya zama cikin zũciyar mutum mai ibãda da gaskiya. Ibãda ta gaskiya ita ce wadda aka yi ta kamar yadda Allah Ya ce a yi ta. Banda ibãdar bidi'a, ba ta korar Shaiɗan. Kuma da sharaɗin a yi ibãdar da kyakkyawar niyya, dõmin aikin da bãbu niyya mai kyãwu game da shi ɓãtacce ne.

5. "Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane."

6. "Daga aljannu da mutane."

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'falaq