Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Al'shams: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 91 a Mushafi, ayoyi 15, tana farawa a shafi na 595.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'baladSura Al'lail ›

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.

2. Kuma da wata idan ya bi ta.

3. Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.

4. Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.

5. Da sama da abin da ya gina ta.

6. Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.

7. Da rai da abin da ya daidaita shi.

8. Sa'an nan ya yi masa Ilhamar fãjircinsa da shiryuwarsa.

9. Lalle ne wanda ya tsarkake[1] shi (rai) ya sãmi babban rabo.

[1] Karɓar imãni da aiki da abinda ya ƙunsa tsarkake rai ne.

10. Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe[1] shi (da laifi) ya tãɓe.

[1] Kãfirci turbuɗe rai ne da zunubi.

11. Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.

12. A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).

13. Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"

14. Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).

15. Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'baladSura Al'lail ›