Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Al'ifidar: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 82 a Mushafi, ayoyi 19, tana farawa a shafi na 587.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'takweerSura Almudaffifeen ›

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. Idan sama ta tsãge.

2. Kuma idan taurãri suka wãtse.

3. Kuma idan tẽkuna aka facce su.

4. Kuma idan kaburbura aka tõne su.

5. Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.

6. Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci.

7. Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.

8. A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.

9. A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!

10. Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.

11. Mãsu daraja, marubũta.

12. Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.

13. Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.

14. Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.

15. Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.

16. Bã zã su faku daga gare ta ba.

17. Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa ranar sakamako?

18. Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?

19. Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'takweerSura Almudaffifeen ›